
Hukumar asusun adashen gat ana fansho na jiha da kananan hukumomin jihar Jigawa ya ce ma’aikatan gwamnati 100 ne suka mutu a cikin wata guda a jihar Jigawa.
Sakataren zartarwa na hukumar, Kamilu Aliyu Musa ne ya bayyana haka a lokacin da yake zantawa da manema labarai game da biyan kudaden fansho da hakkin mamata a ofishin sa.
Ya ce hukumar ta biya naira biliyan 1 da miliyan 215 ga mutane 550 da suka yi ritayi a matsayin fansho na watan Yuli da muke ciki.
Kamilu Musa ya bayyana cewa wadanda aka biya kudaden, an kasasu kashi hudu domin biyansu hakkokinsu.
Sakataren zartaswar ya kuma jaddada alkawarin hukumar na biyan kowane ma’aikacin gwamnati da ya yi ritaya hakkokinsa a cikin wata daya da barin aiki.
Daga nan sai ya yabawa Gwamna Muhammad Badaru Abubakar bisa goyon bayan da yake baiwa hukumar tare da sakin kudaden fansho a lokacin da ya dace.