Kotu ta yankewa makashin Hanifa hukuncin kisa

67

Wata babbar kotun Kano a yau ta yankewa Abdulmalik Tanko da Hashimu Isyaku hukuncin kisa ta hanyar rataya bisa samunsu da laifin yin garkuwa da kuma kashe wata dalibar Noble Kids Academy mai suna Hanifa Abubakar ‘yar shekara biyar.

A ranar 14 ga watan Fabrairu ne gwamnatin jihar Kano ta gabatar da tuhume-tuhume biyar da suka hada da hada baki, yunkurin yin garkuwa da mutane, yin garkuwa da mutane da kuma boye gawa kan Abdulmalik Tanko, Hashimu Isyaku da Fatima Musa.

A hukuncin da ya yanke, Mai shari’a Usman Na-Abba, ya yanke wa wanda ake kara na farko, Abdulmalik Tanko hukuncin kisa ta hanyar rataya da kuma shekara biyar bisa samunsa da laifin hada baki.

Ya kuma yanke wa wanda ake kara na biyu, Hashimu Isyaku, hukuncin kisa ta hanyar rataya, da kuma shekaru biyu bisa samunsa da laifin yunkurin yin garkuwa da mutane da kuma shekara biyu bisa laifin hada baki.

Kotun ta kuma yanke hukuncin daurin shekaru biyu ga wacce ake kara ta uku, Fatima Jibrin, bisa laifin yunkurin yin garkuwa da mutane da hada baki.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

19 + 13 =