Hukumomin leken asiri sun bani kunya – Buhari

67

Shugaban kasa Muhammadu Buhari a jiya ya ziyarci gidan yarin Kuje da ‘yan ta’adda suka kai wa hari, inda ya nuna rashin jin dadinsa kan tsarin leken asirin kasarnan.

Bayan duba wasu wuraren da harin ya shafa, shugaba Buhari ya zanta da manema labarai, inda ya nuna rashin jin dadinsa da tsarin leken asiri da amfani da bayanan leken asiri.

Shugaban kasar yace ya kadu matuka da girman harin.

Shugaban kasar wanda ke kan hanyarsa ta zuwa kasar Senegal, an kuma sanar da shi cewa jami’an tsaro sun kwato fursunoni 350 daga cikin wadanda suka tsere, yayin da aka rasa wasu kimanin 450, kuma ana ci gaba da aikin kamo sauran.

A wani batun kuma, fadar shugaban kasar ta yi watsi da sukar da shugaban kasar ya sha kan tafiyarsa zuwa birnin Dakar na kasar Senegal.

Hakan yazo ne cikin wata sanarwa da kakakin shugaban kasa, Mallam Garba Shehu, ya fitar a jiya.

Shima, da yake gabatar da tambayoyi a harin da aka kai kan ayarin motocin shugaban kasa a ranar Talata a jihar Katsina, mai baiwa shugaban kasa shawara kan harkokin yada labarai, Femi Adesina, ya ce babu wanda ya samu mummunan rauni cikin wadanda ke ayarin motocin kamar yadda ake zato.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

ten + 5 =