Gwamnatin Nasarawa ta rufe dukkanin makarantun jihar

56

Gwamnatin jihar Nasarawa ta bayar da umarnin rufe dukkanin makarantun gwamnati da masu zaman kansu a fadin jihar, nan take, biyo bayan barazanar tsaro a babban birnin tarayya da sauran sassan kasar nan.

Kwamishiniyar ilimi ta jihar Fati Sabo ce ta bayyana hakan a jiya a karshen taron majalisar zartarwar jihar da aka gudanar a birnin Lafia babban birnin jihar.

Fati Sabo ta ce matakin ya zama dole saboda kusancin jihar da babban birnin tarayya da kuma kudurin gwamnatin Gwamna Abdullahi Sule na tabbatar da cewa makarantun jihar Nasarawa suna gudanar da ayyukansu cikin yanayi na tsaro mai kyau.

Kwamishiniyar ta bayyana cewa rufe makarantun bai shafi daliban da ke rubuta jarrabawar kammala sakandare ba, saboda gwamnatin jihar ta sanya matakan da suka dace don tabbatar da tsaron lafiyar su a lokacin jarrabawar.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

15 + 8 =