Gwamnatin Kano ta saki N865m domin biyan tallafin karatu

41

Gwamnatin jihar Kano ta ce ta amince da sakin naira miliyan 865 ga hukumar bayar da tallafin karatu ta jihar domn biyan kudaden tallafin karatu na scholarship ga dalibai a fadin kananan hukumominta 44.

Ta kuma amince da ninka kudaden tallafin karatun ga dalibai ‘yan asalin jihar da ke karatu a makarantu daban-daban a fadin Najeriya.

Kwamishinan yada labarai na jihar, Muhammad Garba, wanda ya bayyana hakan a lokacin da yake zantawa da manema labarai a Kano, ya ce matakin na daga cikin kudurin taron majalisar zartarwar jihar da aka gudanar a jiya.

Muhammad Garba ya bayyana cewar jimillar dalibai dubu 40 da 494 ne za su ci gajiyar tallafin.

Ya kara da cewa, jimillar kudaden tallafin karatu ga daliban cikin gida dubu 40 da 494 daga kananan hukumomi 44 da ke masarautun Karaye, Bichi, Rano, Gaya da Kano a jihar ya kai naira miliyan 836 da dubu 269 da naira 150, yayin da aikin biyan kudaden zai lashe naira miliyan 29 da dubu 180.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

nine + two =