Asusun adashen gata na jiha da kananan hukumomin jihar Jigawa ya kaddamar da biyan hakkokin ma’aikatan da suka rasu a bakin aiki ga magada da kuma cikon kudaden fansho ga magadan ‘yan fanshon da suka rasu alhali basu cika watanni 60 suna karbar fansho ba.
Sakataren zartarwa na asusun, Kamilu Aliyu Musa ya sanar da hakan a lokacin kaddamar da biyan hakkokin magadan da ya tasamma kudi fiye da naira miliyan 295.
Yace daga cikin hakkokin da za a biya akwai na magadan ma’aikatan da suka rasu a bakin aiki a matakin jiha da kananan hukumomi da kuma na sashen ilmin kananan hukumomi su 100 da kudinsu ya tasamma naira miliyan 267.
Kamilu Aliyu ya kara da cewa za a biya cikon kudaden fansho ga magadan ‘yan fanshon da suka rasu alhali basu karbi fansho na watanni 60 ba su 37 da kudinsu ya tasamma naira miliyan 27.
Yace ana biyan hakkokin ma’aikatan da suka rasu da cikon kudaden fanshon bayan magadan sun zo da magatakarda na kotuna sannan kuma asusun ya tantancesu kafin a basu chakin kudaden.