Hukumar kidaya ta kasa a jiya ta ce za ta dauki ma’aikatan wucin gadi miliyan uku domin kidayar jama’a a shekarar 2023.
Kwamishinan hukumar na kasa mai wakiltan jihar Kaduna, Dr Abdulmalik Durunguwa ne ya bayyana hakan a yayin wani taron majalisar gari kan kidayar gwaji na shekarar 2023 a garin Kafanchan dake jihar Kaduna.
Abdulmalik Durunguwa ya ce za a bude shafin internet na daukar ma’aikatan ne a watan Satumba ga masu sha’awar neman aikin.
Ya ce makasudin taron jama’ar garin shi ne wayar da kan jama’a kan kidayar gwaji da za a gudanar a kananan hukumomin Sanga, Jaba da Kachia na mazabar Kaduna ta Kudu.
A cewarsa, kidayar gwajin da za a gudanar har zuwa karshen wata, za ta kasance gwaji ga aikin kidayar jama’a da gidaje na shekarar 2023.
Ya nemi goyon baya da hadin kan masu ruwa da tsaki domin samun nasarar kidayar gwajin.