Gwamnati za ta dasa bishiyoyi miliyan 2 a Jigawa

66

An bukaci malaman gandun daji a jihar Jigawa da su kara kwazo da himma wajen samun nasarar shirin gwamnatin jiha na dashen itatuwa miliyan biyu da za a rabawa al’umma kyauta.

Daraktan Gandun Daji a ma’aikatar kare mahalli ta jiha, Yahaya Uba Kafin-Gana, ya bada wannan shawara a lokacin da ya ziyarci wasu cibiyoyin rainon itatuwa dake sassan jihar.

Yace gwamnatin jiha ta kammala duk wani shiri na dashen itatuwa daban daban da zasu dace da al’umomin jihar.

Yahaya Kafin-Gana ya kuma shawarci kungiyoyin sa kai da sauran kungiyoyi da daidaikun mutane da su marawa kudirin gwamnati baya na ciyar da mahallli gaba.

Ya kuma yabawa kokarin gwamnatin jiha da kungiyoyi da shugabannin al’umma bisa hadin kan da suke bayarwa wajen samun nasarar shirin yaki da kwararowar hamada da zaizayar kasa.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

10 + six =