Gwamnati ta yi kiran a daidaita yawan haihuwa

42

Gwamnatin tarayya ta yi kira da a daidaita yawan haihuwa a kasar nan domin samun ci gaba mai dorewa.

Ministan lafiya Osagie Ehanire ne ya bayyana haka jiya a Abuja a wajen bikin ranar yawan jama’a ta duniya, wanda hukumar kidaya ta kasa ta shirya.

Osagie Ehanire, wanda darakta mai kula da lafiyar iyali, Salma Ibrahim Anas ta wakilta, ya ce zai yi wahala Najeriya ta cimma burinta na ci gaba mai dorewa bisa la’akari da yawan haihuwar da ake yi a kasarnan.

A nasa jawabin, shugaban hukumar kidaya ta kasa, Nasir Isa-Kwarra, ya ce hukumar za ta samar da sahihan bayanan kidaya masu inganci bisa tanadin ka’idojin kasa da kasa.

Da take mayar da martani, wakiliyar hukumar kula da yawan al’umma ta Majalisar Dinkin Duniya, Ulla Mueller, ta ce kasashen Afirka sun dogara da Najeriya wajen taimakawa domin cimma muradun ci gaba mai dorewa a shekarar 2030.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

19 − 3 =