Gwamnati ta amince da biliyan 400 domin rage talauci

71
Muhammadu Buhari

Kwamitin rage talauci da dabarun cigaban kasa ya ce an amince da kudi naira miliyan dubu 400 domin shirye-shiryen rage radadin talauci daban-daban a shekarar 2022.

Gwamna Abdullahi Sule na jihar Nasarawa ya tattauna da manema labarai jiya bayan kammala taron kwamitin rage talauci da dabarun cigaban kasa, a fadar shugaban kasa dake Abuja.

Gwamna Abdullahi Sule ya ce taron an yi shi ne domin duba yadda ake aiwatar da abin da aka amince da shi a kasafin kudi.

Advertisement

Ya ce babban abin da taron yafi mayar da hankali akai shi ne yaba wa kungiyoyin fasaha da suka samu damar hada kai wajen sanar da bukatarsu ta kasafin kudi.

Shugaban kasa Muhammadu Buhari a bara ya kaddamar da kwamitin rage talauci da dabarun cigaban kasa wanda mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo zai jagoranta.

Shugaban ya dorawa kwamitin alhakin fitar da ‘yan Najeriya miliyan 100 daga kangin talauci a cikin shekaru 10.

Advertisement

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

fifteen + 12 =