El-Rufa’i yayi barazanar korar malaman jami’ar KASU dake yajin aiki

58

Gwamna Nasir El-Rufai na jihar Kaduna ya yi barazanar korar daukacin malaman jami’ar jihar Kaduna (KASU) da ke yajin aikin kungiyar malaman jami’o’i (ASUU) a halin yanzu.

Kungiyar ASUU dai ta shiga yajin aikin ne tun a watan Fabrairu saboda gazawar gwamnati wajen biyan bukatunsu.

Duk kokarin da aka yi na mayar da malaman ajujuwa ya ci tura.

A ranar Litinin ne kungiyoyin kwadago suka fara zanga-zangar nuna goyon baya ga kungiyar ASUU.

Amma da yake magana jita ta wani shirin rediyo a Kaduna, Nasir El-Rufai ya bukaci malaman da su koma ajujuwa domin gudun kada a kore su daga aiki.

Gwamnan ya ce malaman jami’ar jihar Kaduna ba su da dalilin shiga yajin aikin.

Yace kungiyar ASUU tana da matsala ne da gwamnatin tarayya ba gwamnatin jiha ba.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

four × 3 =