Hukumar da ke yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa, EFCC, ta ce a yau za ta gurfanar da tsohon Akanta Janar na tarayya, Ahmed Idris a gaban kuliya.
Shugaban sashen yada labarai na hukumar EFCC Wilson Uwujaren ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar jiya a Abuja.
Wilson Uwujaren ya ce za a gurfanar da tsohon Akanta Janar na tarayya da sauran mutane uku a gaban mai shari’a Adeyemi Ajayi na babbar kotun babban birnin tarayya.
Ya ce sauran ukun da za a gurfanar tare da Akanta Janar na Tarayya kan almundahanar kudi naira miliyan dubu 109 sun hada da Godfrey Akindele, Mohammed Usman da Kamfanin Kasuwar Kayayyaki ta Gezawa.
A cewarsa, za a gurfanar da wadanda ake zargin ne a gaban kuliya bisa tuhume-tuhume 14 da suka hada da sata da kuma cin amana.
Sawaba Radio ta tunatar da cewa Hukumar EFCC ta kama tsohon Akanta Janar na Tarayya a ranar 16 ga watan Mayu bisa zargin karkatar da kudade naira miliyan dubu 109.