ECOWAS tace ‘yan ta’adda sun kashe mutane 14,000 cikin shekaru 4

36

Kungiyar Tattalin Arzikin Yammacin Afirka ECOWAS ta ce akalla mutane dubu 14 da 500 ‘yan ta’adda suka kashe a yankin Afirka ta Yamma a cikin shekaru hudu da rabi.

Shugaban kungiyar ECOWAS mai barin gado, Jean-Claude Kassi Brou, wanda ya bayyana haka a lokacin bikin mika mulki ga sabon shugaban kungiyar, Dr Omar Alieu Touray, ya ce mutane miliyan 5 da rabi ne kuma suka rasa matsugunansu.

Jean-Claude Brou ya ce hukumar ta kai dauki don ba da taimako ga da yawa daga cikin wadanda suka gamu da iftila’in annoba kala-kala.

Ya bukaci al’ummar yankin da su kasance masu hadin kai tare da bayar da goyon bayansu ga masu gudanar da zabe.

A nasa jawabin bayan karbar ragamar mulki, Omar Touray ya yi kira ga kasashe mambobin kungiyar da su ci gaba da ba hukumar goyon baya ta hanyar tabbatar da biyan kudaden harajin kungiyar da kuma aiwatar da ka’idojin kungiyar ta ECOWAS baki daya.

Ya yi alkawarin sabunta alkawarin yin aiki tukuru domin jin dadin al’umma.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

13 − 4 =