Dan KAROTA ya samu kyautar miliyan 1 saboda kin karbar cin hanci

51

Hukumar kula da zirga-zirgar ababen hawa ta jihar Kano KAROTA ta tabbatar da cafke wasu manyan motoci guda biyu dauke da katan-katan na barasa fiye da dubu biyu.

A wata sanarwa da kakakinta Nabilusi Abubakar ya fitar jiya, KAROTA ta ce giyar ta haura ta naira miliyan 50.

Nabilusi Abubakar ya ce manajan daraktan hukumar, Baffa Babba Dan’agundi, ya kuma baiwa jami’in hukumar da ya kama motocin kyautar naira miliyan 1 bayan ya ki karbar cin hancin naira dubu 500 domin ya saki kayayyakin da ya kama.

Ya ce manajan daraktan ya yabawa jami’in dan kishin kasa tare da kira ga sauran jami’an hukumar da su yi koyi da shi, yana mai kira gare su da su yi la’akari da tsaron rayuka da dukiyoyi da kuma rayuwar jama’ar jihar fiye da komai.

A cewar manajan daraktan, gwamnatin jihar ta haramta shigo da barasa da kuma shan barasa a fadin jihar baki daya.

Ya kuma yi gargadin cewa hukumar KAROTA a karkashin jagorancin sa ba za ta kyale duk wanda aka kama da laifin kawo barasa a jihar ba.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

1 × 4 =