Buhari ya shilla zuwa Senegal

63

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bar Abuja jiya domin halartar taron kungiyar ci gaban kasa da kasa a Dakar, babban birnin kasar Senegal.

Kungiyar ci gaban kasa da kasa wata cibiyar hada-hadar kudi ce ta kasa da kasa wacce ke ba da lamuni mai rangwame da tallafi ga kasashe masu tasowa.

Mai magana da yawun shugaban kasa, Garba Shehu, ya tabbatar da tafiyar Shugaba Buhari a wata sanarwa da ya fitar jiya a Abuja.

A cewarsa, ana sa ran shugaba Buhari zai bi sahun sauran shugabannin kasashen Afirka wajen shiga tattaunawar bude taron akan kalubalen ci gaba da kuma abubuwan da aka sa a gaba.

Shugabannin na Afirka za su kuma tattauna kan shirye-shiryen kawo sauyi da za su haifar da daftarin alkawarukan Dakar.

Shugaban kasar Senegal Macky Sall ne ya karbi bakuncin babban taron da aka shirya gudanarwa a yau.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

4 × 5 =