Buhari ya nemi majalisa ta tabbatar da alkalin alkalan kasa Ariwoola

24

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya rubutawa majalisar dattawa wasika, yana neman a tabbatar da mai shari’a Olukayode Ariwoola a matsayin babban alkalin alkalan kasa.

Olukayode Ariwoola ya kasance mai rikon mukamin alkalin alkalan kasa, bayan murabus din mai shari’a Mohammed Tanko a ranar 27 ga watan Yuni saboda rashin lafiya.

Da yake karanta wasikar shugaban kasar a zaman majalisar na yau, shugaban majalisar dattawa, Ahmad Lawan, ya ce bukatar tabbatar da alkalin alkalan na bisa turbar kudin tsarin mulkin kasarnan.

A wata wasika ta daban da shugaban kasar ya aikewa majalisar dattijai mai dauke da kwanan watan 21 ga watan Yuli, shugaban kasar ya bukaci babban zauren majalisar ya tabbatar da nadin Dr. Suleiman Agha-Afikpo a matsayin kwamishinan da ke wakiltar yankin Kudu maso Gabas, a hukumar alhazai ta kasa.

Ya bayyana cewa bukatar ta zo daidai da tanadin dokar hukumar alhazai ta shekarar 2004.

A wani batun kuma, majalisar dattawa a yau ta tabbatar da Mohammed Bello a matsayin shugaban hukumar tattarawa da rabon kudaden shiga.

Tabbatar da Mohammed Bello ya biyo bayan nazarin rahoton kwamitin tsare-tsare da harkokin tattalin arziki na kasa.

Shugaban kwamitin, Sanata Olubunmi Adetunmbi, a cikin jawabinsa, ya ce daga cikin takardun da ake da su da kuma jawabin da ya yiwa kwamitin, wanda aka nada ya cika sharuddan da ake bukata na nada shi a matsayin shugaban hukumar tattarawa da rabon kudaden shiga.

Ya bayyana cewa babu koke a kan wanda aka nada; sannan kuma babu wani korafi daga sanatocin jiharsa ta asali da aka samu akan nadin nasa.

A saboda haka majalisar ta dattawa ta tabbatar da nadin nasa bayan amfani da rahoton kwamitin.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

three × three =