Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana cewa babban abin da zai barwa ‘ya’yansa gado shi ne ilimi, inda ya jaddada cewa kada su yi tsammanin samun wani abu a matsayin gado.
Mai magana da yawun shugaban kasar, Garba Shehu, a wata sanarwa da ya fitar, ya ce shugaban kasar ya bayyana hakan ne a jiya a fadar Sarkin Daura a lokacin bikin Sallah a Daura, jihar Katsina.
A saboda haka shugaban kasar ya bukaci matasa da su nemi ilimi, ba don aikin gwamnati ba, sai dan su yi amfani da ilimi da basira wajen yaki da talauci da biyan bukatun karni na 21.
Ya kuma roki iyaye su koya wa yara dabi’u masu kyau, wadanda suka hada da tsoron Allah mai zurfi, mutunta hukumomi da kuma yin rayuwa mai ma’ana ta hanyar ci gaba da neman ilimi.
Ya ce ya kamata a ba da karin lokaci wajen horar da shugabannin da za su jagoranci al’umma nan gaba, tare da sanin asali na kyawawan dabi’u, saboda duniya mai saurin canzawa ta hanyar amfani da sabbin fasahohi.