Shugaban kasa Muhammadu Buhari a jiya ya bukaci ‘yan kungiyar ASUU da su sake duba matsayar su kan yajin aikin da suke yi, yana mai cewa ya isa haka.
Shugaban kasar ya nuna damuwarsa kan cewa yajin aikin zai haifar da illa ga iyalai da tsarin ilimi da kuma ci gaban kasar nan.
Mai taimaka wa shugaban kasa kan harkokin yada labarai, Malam Garba Shehu, ya bayyana cewa shugaba Buhari ya yi wannan kiran ne a lokacin da ya karbi bakuncin wasu gwamnoni da ‘yan majalisar da shugabannin siyasa na jam’iyyar APC a gidansa da ke Daura a jihar Katsina.
Maziyartan sun je Daura ne domin yi wa shugaban kasa barka da Sallah.
Shugaba Buhari ya bayyana cewa yajin aikin ya riga ya yi tasiri kan iyaye da dalibai da sauran masu ruwa da tsaki, lamarin da ya jawo matsaloli da dama da ke neman a magance.
Ya lura cewa makomar Najeriya ta dogara ne kan ingancin ilimi.
Ya ba da tabbacin cewa gwamnati ta fahimci matsayin kungiyar, amma ya kamata a ci gaba da tattaunawa da dalibai a ajujuwa.