An yi hasashen ruwan sama ranar Sallah a wasu jihohin Arewa

88

Hukumar Kula da Yanayi ta Kasa ta yi hasashen samun yanayin hadari da hasken rana daga gobe zuwa Asabar.

Hasashen yanayi na hukumar da aka fitar a Abuja ya yi hasashen za a samu gajimare a gobe tare da hasken rana jifa-jifa a yankin arewa tare da yiyuwar samun tsawa a wasu sassan jihohin Adamawa, Bauchi, Taraba, Kaduna, Kano, Kebbi, Zamfara, Sokoto da Borno da yammacin ranar.

Hukumar ta yi hasashen cewa yankin Arewa ta tsakiya zai kasance cikin yanayin gajimare tare da yiwuwar samun tsawa a jihohin Neja, Kogi, Abuja, Filato da Nasarawa da rana.

A cewar hukumar, ana sa ran samun gajimare da hasken rana jifa-jifa a yankin arewacin kasar a ranar Asabar da safe inda ake sa ran samun tsawa a jihohin Borno, Adamawa da Taraba da safe.

Hukumar ta yi hasashen tsawa a wasu sassan jihohin Borno, Yobe, Jigawa, Kaduna, Kebbi da Zamfara da yammacin ranar.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

17 − 7 =