Tsohon Firayim Ministan Japan Shinzo Abe ya fadi bayan da aka harbe shi a wani biki a birnin Nara.
An harbi Shinzo Abe sau biyu, inda harbin na biyu ya same shi a bayansa, lamarin da ya sa ya fadi kasa.
Tsohon gwamnan Tokyo Yoichi Masuzoe ya fada a cikin wani sakon twitter cewa Shinzo Abe mai shekaru 67 yana cikin mawuyacin hali.
Hotunan bidiyo da ke yawo a shafukan sada zumunta, wadanda ba a iya tantance su ba, sun nuna ma’aikatan jinya sun zagaye Shinzo Abe a tsakiyar titi.
Shinzo Abe yana ba da jawabi ga wani dan takara a Nara lokacin da harin ya faru. Shaidun gani da ido sun ce sun ga wani mutum dauke da abin da suka bayyana a matsayin babbar bindiga.
Harbin farko bai same shi ba amma harbin na biyu ya samu Shinzo Abe a baya. Nan take ya fadi kasa yana zubar da jini. Daga nan ne jami’an tsaro suka tsare maharin wanda bai yi yunkurin guduwa ba.