An gano ma’aikatan da aka yiwa karin girma ba bisa ka’ida ba a Jigawa

392

Kwamitin tantance ma’aikata na jihar Jigawa, ya gano wasu ma’aikata da dama da aka yiwa karin girma ba bisa ka’ida ba a karamar hukumar Yankwashi.

Shugaban kwamitin kuma wakilin mazabar Birnin Kudu a majalisar dokokin jihar Jigawa, Injiniya Surajo Muhammad Kantoga ya sanar da hakan ga jami’in yada labarai na yankin, jim kadan da aikin tantance ma’aikatan yankin.

Yace wasu ma’aikatan an yi musu karin girma sau biyu a shekara, inda yace hakan ya sabawa dokar aiki.

Surajo Muhammad Kantoga ya kara da cewar kwamitin ya sake gano wasu ma’aikatan da su ka yi ritaya daga aiki shekara da shekaru amma albashinsu yana fitowa a kowane wata.

Ya shawarci ma’aikatan jihar nan dasu sanya tsoran Allah da kuma bin doka da oda wajen gudanar da ayyukansu.

A nasa jawabin, shugaban karamar hukumar, Mubarak Ahmed ta hannun daraktan ma’aikata, Shehu Usman Aliyu, ya godewa kwamitin bisa gudanar da aikin.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

2 − 2 =