A shirye muke mu janye yajin aiki – ASUU

68

Kungiyar malaman jami’o’i (ASUU) tace a shirye take ta janye yajin aikin da take yi.

ASUU ta fara yajin gargadi a ranar 14 ga watan Fabrairu domin a biya mata bukatunta.

Kungiyar daga baya ta ayyana tafiya cikakken yajin aiki, inda ta zargi gwamnatin tarayya da rashin gaskiya.

Advertisement

A wata fira ta gidan talabijin na Channels, shugaban kungiyar ASUU, Farfesa Emmanuel Osodeke yace kungiyar na jiran samun martani mai kyau daga gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Emmanuel Osodeke yace gwamnati ta kasa biyan albashi ga malaman jami’ar dake yajin aiki, tsawon watanni 5.

Kungiyar malaman jami’o’i ta ASUU tana takun saka da gwamnatin tarayya, inda take kafa hujjar cewa gwamnati ta kasa cika alkawarukan da ta daukarwa kungiyar a shekarar 2009.

Advertisement

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

ten + six =