Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Sa’ad Abubakar, na uku, a jiya ya umurci al’ummar Musulmi da su fara duba jinjirin watan Muharram daga yau.
Ganin jinjirin wata, bisa la’akari da kalandar Hijira, yana nuna shigowa sabuwar shekarar Musulunci ta 1444 bayan hijira.
Muharram shi ne watan farko na kalandar Musulunci kuma ana daukarsa a matsayin wata mai alfarma.
Alhaji Sa’ad Abubakar wanda kuma shi ne Shugaban Majalisar Koli ta Harkokin Addinin Musulunci ta Najeriya ya ba da umarnin a cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun Shugaban Kwamitin ba da shawara kan harkokin addini, Farfesa Sambo Junaidu.
Sarkin Musulmin ya roki Allah SWT da ya taimaki al’ummar Musulmi wajen gudanar da ayyukansu na addini.