Za a kaddamar da Qur’anin da aka fassara zuwa Igbo

45

Wata kungiyar Musulman Kudu maso Gabas mai suna Kungiyar Da’awah ta Musulmai ‘yan kabilar Igbo, za ta kaddamar da Alkur’ani mai tsarki da aka fassara zuwa harshen Igbo a ranar Juma’a.

Da yake zantawa da manema labarai a yau, wakilan kungiyar karkashin jagorancin Muhammed Murtala Chukwuemeka, sun ce shi da tawagarsa sun yanke shawarar isar da sakon Allah SWT ga ‘yan’uwansa Igbo ta hanyar Alkur’anin da aka fassara.

Muhammed Chukwuemeka, dan asalin karamar hukumar Orlu ta jihar Imo, ya bayyana addinin musulunci a matsayin addinin zaman lafiya da ya haramta kashe ‘yan adam. Ya ce aikin ya dauki shekaru biyar kafin a kammala.

Ya yi kira ga ‘yan Najeriya masu kishi da su halarci taron kaddamar da Qur’anin, wanda za a yi bayan sallar Juma’a a masallacin Ansar-ud-deen da ke Maitama, Abuja.

Muhammed Chukwuemeka ya kuma yi kira ga ’yan Najeriya masu kishin kasa da su tallafa wajen samar da littafin mai tsarki domin isar da sakon Allah cikin lumana ga ’yan kabilar Igbo a Kudu maso Gabas da sauran sassan Najeriya.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

twenty − four =