Wike ne zai gaji Atiku – Sule Lamido

95

Tsohon gwamnan jihar Jigawa kuma jigo a jam’iyyar PDP, Alhaji Sule Lamido ya ce gwamnan jihar Rivers, Nyesom Wike ne zai zama shugaban kasa bayan dan takarar jam’iyyar a zaben 2023, Atiku Abubakar, ya sauka daga Mulki.

Hakan na zuwa ne bayan Sule Lamido ya bayyana gwamnan a matsayin wani kadara ga jam’iyyar PDP kuma jigon da ya shahara wajen aiki, idan aka yi la’akari da yadda ya yi a matsayinsa na gwamnan jihar mai arzikin man fetur.

Sule Lamido wanda ya bayyana hakan a wata zantawa da yayi da manema labarai a gidansa da ke Abuja sai dai ya zargi wasu da bai bayyana sunayensu ba na kusa da gwamnan da rura wutar matsalolin da Nyesom Wike ke magana akai ‘yan kwanakinan, yana mai jaddada cewa dole ne jam’iyyar ta kubutar da gwamnan na jihar Ribas tare da adana shi domin gaba.

A cewar tsohon Ministan Harkokin Wajen, duk wani goyon baya da Nyesom Wike ya bawa PDP a yau, hakki ne na jam’iyyar, inda ya ce jam’iyyar ce ta yi shi ba shine ya yi ta ba.

A wani labarin kuma, Tsohon Gwamna Ayodele Fayose na jihar Ekiti ya bukaci mulkin kasarnan ya koma yankin Kudu, yana mai cewa ba daidai ba ne dan Arewa ya hau mulki bayan Shugaba Muhammadu Buhari ya shafe shekaru takwas.

Ayodele Fayose, na hannun damar Gwamna Nyesom Wike na jihar Ribas, na cikin wadanda suka fafata a zaben neman tikitin takarar shugaban kasa na jam’iyyar adawa, wanda tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar ya lashe.

Bayan kammala zaben fidda gwanin, jam’iyyar PDP ta yi kira ga duk masu ruwa da tsaki a jam’iyyar da su hada kai domin kokarin kwace mulki daga hannun jam’iyyar APC.

Sai dai jam’iyyar PDP ta fara fuskantar rikicin bayan zaben fidda gwani bayan Atiku Abubakar ya zabi Gwamna Ifeanyi Okowa na jihar Delta a matsayin dan takarar mataimakinsa.

Atiku Abubakar ya zabi Ifeanyi Okowa a kan Nyesom Wike duk da shawarar da wasu shugabannin jam’iyyar suka bayar.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

18 − thirteen =