Mutane tara sun mutu a hatsarin mota a Gombe

54

Hukumar kiyaye hadurra ta kasa a jihar Gombe ta tabbatar da mutuwar mutane tara a wani hatsarin mota da ya afku a jihar.

Kwamandan hukumar a jihar Gombe, Felix Theman, wanda ya tabbatar wa kamfanin dillancin labarai na kasa hatsarin a jiya, ya ce hatsarin ya afku ne a mahadar Bomala da misalin karfe 8 da mituna 40 na dare.

Felix Theman ya ce hatsarin ya faru ne sakamakon tsinkewar birki daga wata tirela mai dauke da galan-galan na man girki.

A cewarsa, mutane 20 ne hatsarin ya shafa, inda 11 suka samu raunuka daban-daban.

Ya ce an kai wadanda suka jikkata zuwa Asibitin kwararru na Gombe da Asibitin Koyarwa na Tarayya da ke Gombe domin yi musu magani.

Ya kuma ce an ajiye gawarwakin mutanen bakwai da suka mutu a dakin ajiyar gawa na Asibitin kwararru yayin da sauran gawarwaki biyun kuma an ajiye su a dakin ajiyar gawa na asibitin koyarwa na gwamnatin tarayya da ke Gombe.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

sixteen − seven =