Mozambique ta zama wakiliya a kwamitin sulhu na MDD

37

Majalisar Dinkin Duniya ta zabi kasar Mozambique a matsayin wakiliyar da ba ta dindindin ba, a kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya na wa’adin shekaru biyu, wanda zai fara daga watan Janairu.

Sauran kasashen da aka zaba a zaben na jiya sune Ecuador, Japan, Malta da kuma Switzerland.

Kasashen za su maye gurbin Indiya, Ireland, Kenya, Mexico da Norway.

Shugaban kasar Mozambique Filipe Nyusi ya ce kasar za ta zama muryar kasashen Afirka da ke neman kafa makoma mai kyau da zaman lafiya.

Mozambique ta samu kuri’u 192, Ecuador ta samu 190, Japan ta samu 184, Malta ta samu 185, sai Switzerland da ta samu 187.

Majalisar mai wakilai 15 tana da wakilai biyar na dindindin da suka hada da Amurka da Birtaniya da Faransa da Rasha da China, sai wakilai 10 wadanda ba na dindindin ba.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

sixteen + two =