Masallacin Harami ya samu kwafi 80,000 na Qur’ani domin rabawa mahajjata

40

An samar da sabbin kwafin kur’ani mai tsarki dubu 80, a Babban Masallacin Harami na kasar Saudiyya, gabanin gudanar da aikin Hajjin bana.

Babban daraktan cibiyar kula da kur’ani mai tsarki Ghazi al-Thibani, ya bayyana cewa daga cikin adadin, akwai sabbin kwafin kur’ani mai tsarki na makafi, da kwafin tafsirin ma’anonin kur’ani mai tsarki a harsuna daban-daban, ciki har da Ingilishi, Urdu da Indonesian.

Al-Thibani ya kara da cewa hukumar ta shirya wani shiri na musamman na taya mahajjata murna, inda za ta bayar da kyautar kwafin kur’ani mai tsarki ga kowane mahajjaci, baya ga wani shiri na ma’anonin kur’ani mai tsarki tare da tarjama cikin harsuna sama da 60.

A halin da ake ciki, Saudiyya ta sanar da haramtawa maniyyata tafiya da abubuwa 15 zuwa kasar da nufin gudanar da aikin Hajji.

Wata sanarwa da ma’aikatar aikin Hajji da Umrah ta Saudiyya ta fitar, ta bayyana cewa haramtattun kayayyaki sun hada da reza, wukake, almakashi, kusoshi, guduma, harsashi, bindiga, abu mai guba da sauransu.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

four × five =