Majalisar dattawa ta tantance wadanda za a nada ministoci

51

Majalisar Dattawa ta tantance mutane 7 da za a nada ministoci wadanda shugaban kasa Muhammadu Buhari ya aika da sunayensu domin tabbatar da su.

Mutanen wadanda suka samu rakiya zuwa majalisar kasa daga iyalai da magoya baya, majalisar ta dattawa ta tantance su daya bayan daya a zauren majalisar.

Shugaban kasa Muhammadu Buhari cikin wata wasika mai dauke da kwanan watan 15 ga watan Yunin da muke ciki, ya bukaci majalisar dattawa da ta tabbatar da mutanen 7 da zai nada ministoci.

Yace ya bika bukatar tantancesu bisa tsarin tanadin sashe na 147 karamin sashe na biyu na kundin tsarin mulkin kasarnan na 1999, wanda aka yiwa gyara.

Wadanda aka tantance sune Henry Ikechukwu Ikoh daga jihar Abia; Umana Okon Umana daga jihar Akwa Ibom; Ekumankama Joseph Nkama daga jihar Ebonyi; da Goodluck Nanah Opiah daga jihar Imo.

Sauran sune Umar Ibrahim El-Yakub daga jihar Kano; Ademola Adewole Adegoroye daga jihar Ondo; da kuma Odum Udi daga jihar Rivers.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

20 − thirteen =