Kwankwaso yaje ziyarar ta’aziyyar wadanda aka kashe a cocin Owo

26

Dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar NNPP, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, ya kai ziyarar jaje ga al’ummar jihar Ondo bisa harin da aka kai wa cocin katolika ta Saint Francis.

Sama da masu ibada 40 ne aka kashe a lokacin da ‘yan ta’adda suka mamaye cocin makonni biyu da suka wuce.

Rabiu Kwankwaso yayin ziyarar, ya yi kira ga gwamnatin tarayya da ta kara kaimi wajen tabbatar da tsaron rayuwar ‘yan Najeriya da mazauna kasar, ya kara da cewa ya kamata harkar tsaro ta kasance kan gaba.

Da yake jawabi a fadar Olowo na Owo da Ojomo na Ijebu, tsohon Ministan Tsaron ya yabawa gwamnan jihar Ondo kan kudirinsa na inganta harkar tsaro a jihar.

Wata sanarwa da mai taimaka wa dan takarar shugaban kasan kan harkokin yada labarai Saifullahi Hassan ya fitar, ya ce Rabiu Kwankwaso ya kuma ziyarci wurin da harin ya faru tare da jajantawa mazauna yankin.

Yayin da yake addu’ar Allah ya kawo mana zaman lafiya a kasar nan, Rabi’u Kwankwaso ya yi addu’ar Allah ya jikan wadanda suka rasu.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

twenty − 4 =