Wata kotun tafi da gidanka a Kano ta baiwa FirstBank da Ecobank da Unity Bank wa’adin mako biyu su biya gwamnatin jihar Kano kudaden da ake biya na rijistar kasuwanci, ko kuma a rufe su.
Kotun tafi da gidanka karkashin jagorancin babban alkalin kotun, Ibrahim Gwadabe, ta yanke wa bankunan uku hukuncin kan kin biyan gwamnatin jihar kudaden rijistar kasuwanci karkashin ma’aikatar kasuwanci da ma’adanai ta jihar.
Laifin a cewar alkalin ya ci karo da sashe na 8 da na 9 kuma yana da hukunci a karkashin sashe na 14 na dokar rajistar kasuwanci ta jihar Kano ta shekarar 2014.
Mai magana da yawun ma’aikatar, Sa’adatu Sulaiman ta ce, alkalin kotun ya umarci bankunan uku da su biya kudaden da a cikin makwanni biyu ko kuma a rufe su har sai sun biyan kudaden.
Idan dai ba a manta ba a shekarar da ta gabata ne hukumar tattara kudaden shiga ta jihar Kano ta rufe rassa guda biyar na bankin Guaranty Trust da ke Kano bisa rashin biyan haraji ga gwamnatin jihar.