An fara jigilar maniyyata aikin hajjin bana karon farko a Maiduguri tare da mahajjata 546.
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kaddamar da jigilar mahajjatan a jiya a filin jirgin sama na Maiduguri.
Shugaban kasar wanda ya samu wakilcin Gwamna Babagana Zulum, ya ce shawarar da aka yanke na zaben Maiduguri domin kaddamar da jigilar alhazan na nuni da farin cikin dawowar zaman lafiya a jihar.
Shugaban ya yabawa gwamnatin jihar Borno bisa tallafin da take bai wa hukumar alhazai ta kasa, inda ya kara da cewa gwamnatin tarayya ta samar da kayan aikin da suka dace domin saukaka gudanar da aikin Hajji.
A nasa jawabin, shugaban hukumar alhazai ta kasa, Zikirullah Kunle-Hassan ya godewa gwamnatin tarayya bisa goyon bayan da take baiwa hukumar duk da takaitaccen lokacin da aka bayar na shiryawa da kuma tsara aikin Hajjin.