Gwamnati ta umarci kafafen sadarwa na internet da su ke goge abubuwan badala

64

Gwamnatin Tarayya ta umarci manhajojin sadarwa na intanet, irin su Twitter, WhatsApp, Facebook, Instagram, da TikTok da su tabbatar sun cire ko kuma toshe hanyoyin shiga duk wani abun da bai dace ba, wanda ke nuna tsiraici ko badala da batsa a cikin awanni 24.

An bayar da wannan umarni cikin ka’idojin aiki da aka fitar domin manhajojin sadarwa na intanet.

Bisa ga daftarin ka’idojin, wadandan manhajoji dole ne su yi aiki da sauri don cirewa ko toshe damar yin amfani da abubuwan da ba a yarda da su ba wadanda ke fallasa tsiraicin mutum ko badala da batsa da aka wallafa domin musgunawa, bata suna, ko tsoratar da mutum. Dole ne manhajojin su tabbatar da karbar korafi tare da goge abubuwan cikin sa’o’i 24.

Ka’idojin aikin sun kuma bayar da umarnin ga wadannan manjoji su sauke duk wani abun da bai dace ba, muddin wanda aka ci zarafin ya shigar da korafi ko wata hukuma ta bukaci hakan.

Hukumar bunkasa fasahar sadarwa ta kasa (NITDA) ce ta sanar da fitar da ka’idojin aikin a ranar Litinin.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

12 + two =