Guguwa ta lalata gidaje 100 a jihar Jigawa

97

Guguwar mai karfi ta lalata gidaje kusan 100 a karamar hukumar Gwiwa da ke jihar Jigawa.

Shugaban sashen cigaban al’umma na karamar hukumar Yusif Abdullahi ne ya bayyana haka a lokacin da yake zagayawa da shugaban karamar hukumar a rangadin tantance wuraren da abin ya shafa.

Ya bayyana faruwar lamarin a matsayin qaddara, kuma ya tausayawa wadanda abin ya shafa.

Shugaban karamar hukumar, Sale Ahmad Zauma, ya yi alkawarin cewa majalisar karamar hukumar za ta taimaka wa wadanda abin ya shafa, ya kuma sha alawashin kai rahoton lamarin ga hukumar ba da agajin gaggawa ta jihar domin samun taimako.

A nasa jawabin, dan majalisar wakilai mai wakiltar mazabar Gwiwa a majalisar dokokin jiha, Alhaji Aminu Zakari ya bada tabbacin cewa gwamnatin jihar a shirye take ta taimakawa wadanda lamarin ya shafa.

Hakazalika, mutum daya ya mutu yayin da wasu bakwai suka jikkata sakamakon wata guguwa mai karfi a Tsangayar Mallam Musa Aujara da ke karamar hukumar Jahun a jihar Jigawa.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

four × two =