Ban zabi kowa a matsayin dan takarar shugaban kasa ba – Buhari

47

Shugaban kasa Muhammadu Buhari a jiya ya bayyana cewa bai zabi kowa ba a matsayin dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC.

Idan za a iya tunawa dai, shugaban jam’iyyar APC na kasa, Abdullahi Adamu, ya bayyana shugaban majalisar dattawa, Ahmad Lawan, a matsayin dan takarar shugaban kasa da jam’iyyar ta amince da shi.

Sai dai a lokacin da yake jawabi ga gwamnonin Arewa 14 a karkashin jam’iyyar APC a fadar shugaban kasa, shugaba Buhari ya ce a bar wakilai su zabi duk wani dan takarar da suke so a babban taron jam’iyyar APC na kasa da ke gudana.

A jawabin da ya yi wajen zaman ganawarsa gwamnonin a fadar shugaban kasa da ke Abuja, Shugaba Buhari ya ce jam’iyyar na da muhimmanci kuma dole ne a mutunta ‘ya’yanta, saboda suma su ji suna da muhimmanci.

A cewar wata sanarwa da mai taimaka wa shugaban kasa kan harkokin yada labarai, Garba Shehu ya fitar, shugaban kasar ya ce babu wani dan takara da za a kakabawa mutane a jam’iyyar.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

four × 3 =