Babu wanda zai iya cewa shine silar nasarar Buhari – Fadar shugaban kasa

42

Fadar Shugaban kasa a jiya a Abuja, ta ce babu wanda zai iya ikirarin cewa shi kadai ne silar nasarar shugaban kasa Muhammadu Buhari a zaben 2015 da ya gabata.

A cewar wata sanarwa da babban mai taimaka wa shugaban kasa kan harkokin yada labarai Garba Shehu ya sanya wa hannu, fadar shugaban kasar ta ce bai kamata a yi amfani da abinda ya wuce ba wajen neman zabe mai zuwa.

An ruwaito cewa tsohon gwamnan jihar Legas, Bola Tinubu, ya tayar da kura a ranar Alhamis din da ta gabata inda ya yi ikirarin cewa ba dan shi ba, da shugaba Buhari ba zai taba zama shugaban kasa a 2015 ba.

Dan takarar shugaban kasa ya yi wannan ikirarin ne a dakin taro na masaukin shugaban kasa da ke Abeokuta, babban birnin jihar Ogun, lokacin da yake jawabi ga wakilan jam’iyyar APC gabanin zaben fidda gwani na jam’iyyar.

A martaninta, fadar shugaban kasar ta ce ba abin mamaki ba ne, a jajibirin zaben fidda gwani na jam’iyyar APC, a samu wadanda suka tsaya takara a matsayin ’yan takara da ke son alakanta kansu da nasarar shugaban kasa shekaru bakwai da suka wuce.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

four × 3 =