An tsare Ekweremadu a Ingila bisa laifin daukar sassan jikin mutum

37

Tsohon Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Ike Ekweremadu da matarsa, Béatrice Ekweremadu, da ake tuhumar su da laifin hada baki domin daukar sassan jikin wani yaro a kasar Burtaniya, za su fuskanci daurin rai da rai idan aka same su da laifi a karkashin dokar bautar zamani ta Burtaniya ta shekarar 2015.

Ma’auratan, wadanda aka kama bayan wani bincike da tawagar kwararrun masu bincike na ‘yan sandan London suka gudanar, an gurfanar da su a gaban kotun majistare ta Uxbridge.

Kotun ta hana su beli, amma ta bayar da umarnin a ci gaba da tsare su har zuwa ranar 7 ga watan Yuli.

Rundunar ‘yan sandan ta ce an kaddamar da binciken ne bayan an sanar da masu bincike dangane da laifin, wanda ya sabawa dokar bautar zamani a watan Mayun 2022.

A halin da ake ciki, akwai wata takarda da ake yadawa a kafafen sada zumunta da ke nuna cewa, Ike Ekweremadu, a watan Disamba 2021, ya rubuta wasika ga ofishin jakadancin Burtaniya game da bayar da gudummawar koda ga ‘yar sa.

Ba a samu jin ta bakin mai magana da yawun Ike Ekweremadu, Uche Anichukwu, ba.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

3 × 4 =