An kashe mayaka 40 a hare-haren jiragen sama marasa matuka a Jamhuriyar Nijar

53

Jiragen saman Faransa sun kashe kimanin mayaka 40 da ke tafiya kan babura a kusa da iyakar Nijar da Burkina Faso.

A wata sanarwa da ta fitar, hukumar sojin Faransa ta kira harin a matsayin sabuwar nasara ta dabara ga yunkurin Faransa na yaki da ta’addanci a yankin Sahel na Afirka.

Hare-haren na jirgin mara matuki a jamhuriyar Nijar na zuwa ne daidai lokacin da kasar Faransa ta sake tsara ayyukan sojojinta a yankin Sahel mai girma a kudu da hamadar sahara inda a baya ta yi mulkin mallaka kuma har yanzu akwai alaka mai karfi ta fuskar tattalin arziki.

Jamhuriyar Nijar ta zama babbar aminiyar Faransa bayan juyin mulkin da sojoji suka yi na hambarar da zababbun shugabanin kasashen Mali da Burkina Faso bisa tafarkin dimokuradiyya, a shekaru biyu da suka gabata.

A farkon wannan shekara ne Faransa ta sanar da janye daukacin dakarunta daga Mali shekaru tara bayan da sojojin Faransa suka jagoranci yunkurin fatattakar kungiyoyin da ke dauke da makamai daga Timbuktu da wasu cibiyoyi a arewacin Mali.

Faransa ta ce tana shirin mayar da dakarunta daga Mali zuwa wasu kasashen yankin Sahel ciki har da Jamhuriyar Nijar.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

one × two =