Amira Safiyan na da tabin hankali – ‘Yansanda

103

Jami’in dansandan James Idachaba na rundunar ‘yansandan babban birnin tarayya yace Amira Safiyan wacce ta shirya garkuwa da kanta, tana da tabin hankali.

James Idachaba ya sanar da haka a yau bayan mai shari’a Chukwuemeka Nweke ya zartar da hukunci biyo bayan amincewa da laifinta da Amira Safiyan ta yi.

Tunda farko kotun ta sake ta bisa wasu sharudda bayan an gurfanar da ita da laifin bayar da labarin karya da nufin yaudarar jama’a.

Bayan ta amince da laifinta, kotun ta zayyana wasu sharudda uku na sakinta.

Kotun ta yanke hukuncin cewa dole ta kasance bisa kulawa na tsawon watanni 12 kuma dole wani mutum ya tsaya mata wanda shine mahaifinta da zai amince da yarjejeniyar cewa zai tabbatar Amira Safiyan tana da tarbiyya.

Kari bisa haka, kotun ta zartar da hukuncin cewa dole Amira Safiyan ta kasance bisa kulawar ‘yarsanda, mataimakiyar kwamishinan ‘yansanda Hauwa Ibrahim, wacce za take sa ido akan jin dadinta da lafiyar kwakwalwarta.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

8 + six =