Uganda tace za ta janye dakarunta daga Congo

41

Hukumar sojin Uganda ta ce za ta janye daruruwan sojojin da ta aika a bara domin taimakawa makwabciyarta Jamhuriyar Dimokaradiyyar Kwango wajen yakar ‘yan tawaye.

Kwamandan sojojin kasa na Ugandan ya ce an yi niyyar gudanar da aikin na tsawon watanni shida ne kawai kuma za a kawo karshensa nan da wata mai zuwa matukar ba a amince da karin wa’adin ba.

Hukumomi a Jamhuriyar Dimokaradiyyar Kwango sun ce sharudda da kuma lokacin ficewar Ugandan na bukatar amincewar kasashen biyu.

A watan Disamba, Uganda ta aike da sojoji dubu 1 da 700 domin shiga aikin hadin gwiwa da dakarun Kongo kan kungiyar ‘yan tawaye da aka fi sani da ADF

Ana zargin kungiyar ‘yan tawayen da kai hare-hare da kisan kiyashi a gabashin Jamhuriyar Dimokaradiyyar Kwango da tayar da bam a Uganda.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

8 + 2 =