Shugabannin Rwanda da Congo sun tattauna daidai lokacin da ake zaman dar-dar

52

Shugaban kasar Rwanda Paul Kagame ya tattauna ta wayar tarho da takwaransa na Jamhuriyar Dimokaradiyyar Kwango Félix Tshisekedi tare da shugaban kungiyar Tarayyar Afirka Macky Sall daidai lokacin da ake fama da tashe-tashen hankula a kan iyaka.

Jamhuriyar Dimokaradiyyar Kwango ta zargi Rwanda da goyon bayan ‘yan tawayen M23 a wani sabon fada a gabashin Jamhuriyar Dimokaradiyyar Kwango, zargin da Rwanda ta musanta.

Dubban mutane ne suka tsere daga gidajensu yayin da sojojin Kongo ke fafatawa da ‘yan tawaye a lardin Kivu ta Arewa.

Shugaban kungiyar Tarayyar Afirka Macky Sall ya karfafawa shugaban kasar Angola João Lourenco kwarin gwiwar ci gaba da shiga tsakani kan batun.

Tun da farko Macky Sall ya nuna matukar damuwarsa game da karuwar tashe-tashen hankula a tsakanin kasashen biyu. Inda ya roki a yi tattaunawa domin warware takaddamar.

A makon da ya gabata, Jamhuriyar Demokradiyyar Kongo ta dakatar da zirga-zirgar jiragen sama zuwa kasar Rwanda.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

fourteen + 17 =