NiMET ta yi hasashen ruwan sama na kwana 3 a Jigawa, Kano da wasu jihohi

197

Hukumar hasashen yanayi ta kasa ta shaida wa mazauna babban birnin tarayya Abuja da jihoshin Bauchi da Gombe da Filato da Taraba da Benue da Cross River da Kwara da Neja da kuma jihar Kogi da su shirya samun ruwan sama mai matsakaicin karfi a cikin kwanaki uku masu zuwa.

Hukumar ta kuma yi hasashen samun ruwan a jihohin Jigawa, Yobe, Kano, Lagos, Oyo, Ogun, Ondo, Osun, Ekiti, Kogi, Nassarawa, Edo, Delta, Akwa Ibom, Rivers, Borno, Imo, Abia da kuma jihar Ebonyi daga safiyar yau zuwa yammacin Juma’a.

Hukumar a rahotonta na yanayi da ta fitar jiya ta ce ana sa ran samun ruwan sama kadan a yawancin yankunan arewa maso yamma.

A cewar hukumar, ana sa ran ruwan saman zai kasance tare da iska mai karfi, walkiya da kuma tsawa, don haka akwai yuwuwar faduwar gine-gine masu rauni da rushewar gine-ginen wucin gadi.

Hukumar ta shawarci jama’a da su kasance masu juriya, da kashe na’urorin wutar lantarki kafin lokacin guguwar, kuma su guji tsayawa ko ajiye motoci a karkashin bishiya.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

10 + 18 =