Majalisar Zartarwa ta Tarayya ta amince da sake gina hanyoyi 4

70

Majalisar zartaswa ta tarayya ta amince da naira miliyan dubu 169 da miliyan 700 don sake gina wasu hanyoyi guda hudu a karkashin tsarin karbar haraji.

Ministan ayyuka da gidaje, Babatunde Fashola ne ya bayyana haka a jiya a lokacin da ya ke yiwa manema labarai karin haske game da sakamakon zaman majalisar da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya jagoranta a fadar shugaban kasa da ke Abuja.

A cewar ministar, hanya ta farko da aka bayar a kan wannan tsarin ita ce hanyar Bali zuwa Sheti ta Gashaka zuwa Gembu a jihar Taraba.

Fashola ya kuma bayyana cewa majalisar ta amince da wani kamfani mai zaman kansa da ya zuba jarin sama da naira miliyan dubu 74 domin sake gina wasu hanyoyi guda uku a jihohin Kebbi da Neja.

Ministan yada labarai da al’adu, Alhaji Lai Mohammed wanda ya yi jawabi a madadin takwarorinsa na harkokin sufurin jiragen sama, wutar lantarki da noma, ya ce majalisar ta amince da kimanin naira miliyan dubu 3 da miliyan 500 don siyan kayan aiki Abuja ga ma’aikatar sufurin jiragen sama.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

1 × one =