Kotu ta rufe wanda yake sojan gona a matsayin jami’in tsaron Buhari

55

Hukumar da ke yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa ta EFCC ta gurfanar da wani da ake zargi da damfara mai suna Titus Joshua wanda ya ke sojan gona da cewa shine babban jami’in tsaron shugaban kasa Muhammadu Buhari.

An gurfanar da shi jiya a gaban mai shari’a Shu’aibu na babbar kotun tarayya da ke zama a Benin City.

A wata sanarwa da kakakin hukumar EFCC, Wilson Uwujaren, ya fitar, ya ce an gurfanar da wanda ake zargin ne a kan tuhume-tuhume biyar da suka shafi hada baki da kuma samun kudade ta hanyar yaudara.

Sanarwar ta kara da cewa, ana zargin mutumin da damfarar mutane sama da Naira miliyan 200 da sunan zai taimaka musu wajen samun manyan mukamai a hukumar raya yankin Neja Delta.

Wanda ake tuhumar ya ki amsa laifin da ake tuhumarsa da shi.

Lauyan masu shigar da kara, Ibrahim Mohammed, ya roki Kotun da ta sanya ranar da za a yi shari’a tare da tsare wanda ake kara.

Mai shari’a Shua’ibu ya dage ci gaba da shari’ar har zuwa ranar 30 ga watan Mayun 2022 sannan ya bayar da umarnin tsare wanda ake kara a gidan gyaran da’a.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

3 × 1 =