Jonathan ya karbi fom din takarar shugaban kasa na APC

74

Kimanin sa’o’i 48 da raba kansa daga yunkurin da wasu kungiyoyi ke yi na shigar da shi takarar shugaban kasa a shekarar 2023, a karshe tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan ya yanke shawarar tsayawa takara.

A ranar 9 ga watan Mayu, Goodluck Jonathan ya ki amincewa da karbar fom din tsayawa takarar shugaban kasa da mutane suka saya masa, wadanda aka bayyana a matsayin Fulani makiyaya da kuma almajirai.

An ambato shi yana cewa cin fuska ne mutane su saya masa fom ba tare da amincewar sa ba amma yanzu tsohon shugaban kasa yayi amai ya lashe akan batun.

Wata majiya mai tushe dake da kusanci da Jonathan da ta nemi a sakaya sunanta ta bayyana cewa tabbas tsohon shugaban kasar ya koma jam’iyyar APC ne a hukumance, bayan da ya yi rajista a mazabarsa ta Otuoke da ke jihar Bayelsa.

Majiyar ta bayyana cewa a yau ne ake sa ran Jonathan zai mika form din takarar sa na jam’iyyar APC da ya cike.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

1 × three =