Jirgin sama dauke da mutane 11 ya fado a kusa da Yaoundé a Kamaru

131

Wani karamin jirgin saman fasinja dauke da mutane 11 ya yi hatsari a jiya a wani daji kusa da Yaoundé babban birnin kasar Kamaru.

Ma’aikatar sufurin kasar a cikin wata sanarwa da ta fitar ta ce ba a tabbatar da musabbabin hatsarin ba, amma jirgin ya rasa hanyar sadarwar da masu kula da zirga-zirgar jiragen sama, inda daga bisani aka same shi a cikin dajin da ke da tazarar kilomita 150 a arewa maso gabashin birnin Yaoundé.

Sanarwar ta kara da cewa jirgin ya taso ne daga filin jirgin saman Yaoundé zuwa Belabo da ke gabashin kasar.

Kamfanin dillancin labaran AFP ya rawaito daga majiyoyin gwamnati na cewa wani kamfani ne mai zaman kansa, kamfanin sufurin mai na kasar Kamaru, wanda ke kula da bututun iskar gas da ya ratsa Kamaru da makwabciyarta Chadi.

Majiyar gwamnati ta ce hatsarin ya kasance babban bala’i na farko da ya afku a kasar tun shekarar 2007, lokacin da wani jirgin saman kasar Kenya dauke da mutane 114 ya yi hatsari bayan tashinsa daga filin jirgin Douala.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

2 × 1 =