Jam’iyyar APC ta wanke Gwamna Badaru domin zaben fidda gwani na shugaban kasa

74

Jam’iyyar APC mai mulki ta wanke gwamnan jihar Jigawa Muhammad Badaru Abubakar domin tsayawa takarar zaben fidda gwani na dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar da za a gudanarwa ranar 6 ga watan Yunin gobe.

Kwamitin tantance ‘yan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC karkashin jagorancin John Odigie ya wanke Gwamna Badaru Abubakar a jiya.

A cewar Auwalu Danladi Sankara, mai taimaka wa gwamnan kan harkokin yada labarai, an wanke Gwamna Badaru Abubakar ta hanyar tantance kasancewarsa dan jam’iyya da harkokin kudadensa da kuma takardunsa na karatu, da sauran bukatun dan takarar shugaban kasa kamar yadda kundin tsarin mulkin Najeriya ya tanada.

Tantance gwamnan dai ya kawo karshen cece-kucen da ake yi na cewa ya janye daga takarar domin marawa wani dan takara baya.

Muhammad Badaru Abubakar na daga cikin ‘yan takara 28 da ke neman tsayawa takarar shugaban kasa a jam’iyyar APC a zaben 2023 mai zuwa.

A wani labarin kuma, dan majalisar tarayya mai wakiltar mazabar Kazaure/Roni/Yankwashi/Gwiwa a jihar Jigawa, Muhammad Gudaji Kazaure, ya zargi gwamna Muhammad Badaru Abubakar da shirin yiwa jam’iyyar APC zagon kasa a babban zabe mai zuwa na 2023.

Gudaji Kazaure ya sha kaye a zaben fidda gwani na jam’iyyar APC a hannun shugaban karamar hukumar Kazaure, Mukhtar Zanna.

Gudaji Kazaure a cikin wata sanarwa da ya fitar, ya ce tun da farko ya rubuta takardar koke ga hukumar zabe ta kasa (INEC) kan rashin adalcin da aka yi masa da kuma abin da ya ce ya saba wa dokar zabe a zaben delegates na jam’iyyar.

Dan majalisar ya ce ya aika da koke ga INEC d hedkwatar jam’iyyar APC. Ya yi zargin cewa ba a yi zaben delegates a mazabar tarayya ta Kazaure/Roni/Yankwashi/Gwiwa ba.

Ya ce akasarin delegates da suka kada kuri’a a lokacin zaben fidda gwani, shugaban karamar hukumar Kazaure ne ya bayar da sunayensu ba tare da an gudanar da zabe ba, alhalin shugaban karamar hukumar yana cikin ‘yan takara kuma aka bayyana shi a matsayin wanda yayi nasara a zaben.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

2 + twelve =