Gwamnatin Jigawa za ta dauki malaman makaranta a karkashin shirin J-Teach

119

Gwamnatin jihar Jigawa za ta dauki karin malamai dubu biyu aiki karkashin shirin J-teach a jihar.

Shugaban kungiyar malamai ta kasa (NUT) reshen jihar Jigawa, Comrade Abdulkadir Yunusa Jigawa ne ya bayyana hakan a cikin wani shirin gidan rediyon Jigawa.

Ya ce an dauki matakin ne domin maye gurbin malaman da suka yi ritaya daga bakin aiki da kuma inganta harkar koyo da koyarwa.

Abdulkadir Yunusa ya ce gwamnan jihar Jigawa, Muhammad Badaru Abubakar, ya ba da tabbacin daukan malaman J-Teach 400 zuwa 800 aiki na dindindin.

A cewarsa malamai 900 ne suka yi ritaya daga aiki a bana.

Shugaban kungiyar ta NUT ya ce gwamnatin jihar ta yi ayyuka da dama a fannin ilimi, ta fuskar gyaran fuska da gina sabbin ajujuwa da dakunan gwaje-gwaje da kuma sayen kayayyakin koyo da koyarwa.

Ya ce kungiyar za ta dasa itatuwa dubu a makarantun dake fadin jiharnan.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

20 − 6 =