Gwamnan Lagos ya kakaba dokar hana achaba

46

Gwamnatin jihar Legas ta umurci jami’an tsaro da su aiwatar da dokar hana achaba, saboda ta sanya sabuwar dokar hana zirga-zirgar Babura ba bisa ka’iba ba a jihar.

Gwamna Babajide Sanwo-Olu ya ba da wannan umarnin ne a jiya yayin wata ganawa da kwamishinan ‘yan sandan jihar da kwamandojin yankin da jami’an ‘yansanda na yankuna, a fadar gwamnatin jihar da ke Ikeja.

Sanwo-Olu ya ce an haramta acahaba baki daya a dukkan manyan titunan kananan hukumomin shida na jihar.

Ya ce daga ranar 1 ga watan Yuni, ya kamata jami’an tsaro su aiwatar da dokar haramta achaba a fadin kananan hukumomin da aka lissafa.

Kananan hukumomin da abin ya shafa sun hada da Eti-Osa, da Ikeja, da Surulere, da Legas Island, da Legas Mainland, da kuma Apapa.

A cewarsa, sabon dokar hana achaba ta biyo bayan dokar hana zirga-zirgar baburan haya ta watan Fabrairun 2020.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

17 + six =