Ganduje ya janye daga takarar Sanata a Kano

52

Gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje ya janye daga takarar neman kujerar Sanatan Kano ta Arewa domin kwantar da hankalin abokan hamayyarsa a jam’iyyar APC.

Janyewar Abdullahi Gandue ya share fagen sake takarar Sanata mai wakiltar Kano ta Arewa, Barau Jibrin, daya daga cikin manyan masu kalubalantar Abdullahi Ganduje kan shugabancin jam’iyyar APC a jihar.

Wani jigo a jam’iyyar APC a jihar, Zakari Sarina, wanda ya tabbatar da faruwar lamarin, ya ce an samu fahimtar juna sosai a jam’iyyar.

A baya-bayan nan dai jam’iyyar APC a jihar Kano ta fuskanci ficewar manyan shugabanni zuwa wasu jam’iyyun na siyasa.

Yanzu dai gwamnan ya amince da matsin da yake sha kan ya kyale wasu abokan hamayyarsa irinsu Barau Jibrin su ci gaba da rike mukamansu.

An bayyana cewa, mutanen biyu da wasu jiga-jigan jam’iyyar APC sun yi taro a Abuja inda gwamnan ya janye aniyarsa, domin a samu zaman lafiya a jam’iyyar.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

five × two =